*🏮🎀BABBAN SIRRI🏮🎀*
*NA*
*K.A.S precious hajja ce*👈🏻
*DEDICTED to Ummi ayshat nd pharty b~b*
*Edited by supar star FUTHA LURV😍*
_sakallahu khairan my futha, Allah ya biyaki da alkairi duniya da lahira k'in bani lok'acinki damarki jin daɗ'inki duk dan ki taimake ni so much love you_😘
*4*
Sosai ran Abban Falaq ya ɓ'aci dan a rayuwar shi baya san namiji yana shigar mai gida hakan na matukar ɓ'ata mishi rai,shi kuwa sallau dayake ta uwar masifa yana rantse-rantsen sai Abba ya bashi k'uɗ'in shi ko kuma yanxu su tattara k'ayansu sufita dan yanada waɗ'anda zai saka.
Da sauri Abban Falaq yaja sallau zuwa zaure yafara nunashi da hannu cikin ɓ'acin rai yace mai,"idan har nashiga natarar da matata na kuka wallahi Allah bazan baka k'uɗ'in ba k'uma sai nayi k'ararka sabida k'etare iyaka da k'ayimin", yana k'aiwa nan ya juya ya shiga cik'i, cik'in zafin zuciya.
Hank'alin abba a tashe yak'e domin yau shekara ɗ'aya k'enan da wata uku ɓe bada kuɗ'in haya ba, kasan cewar yau wata tak'was ummin Falaq na k'wance babu lafiya yasa har yanxu ɓe bada ba gashi anzo ana mai tijara.
kuɗ'in da yake tarawa dan saima ummi resting chair su yashiga ɗ'akin ya ɗauko dubu shabiyar ne dama ya kalli inda falaq ta nanike ummi kamar zata koma cikinta,sannan yafita yana kara lissafa kuɗin yaje yabawa sallau dubu goma yanuna mai hanyar fita sannan ya dawo ciki shikuma.
k'arasawa yayi kusa dasu cikin dakewar zuciya yafara magana da tattausar murya.
"Bana san ganin damuwa a gurinku, k'une farin cikina narabu da yan uwana duk sabida ina k'aunarku me yasa yanxu zaku sa damuwa cikin rayuwar ku idan kuka cigaba zaku k'arya min zuciya dan Allah kuyi mana addu'a zata karbu dan baxan iya ganinku cikin k'unci ba ya karasa kamar zaiyi kuka"
Bayan sati biyu anyi hutu a makarantar allon da falaq take zuwa k'asancewar lokacin maulidine k'uma ambata karatun dazatayi a wajan nasu maulud ɗ'in,hak'an yasa hankalin Abbanta ya tashi sabida ko k'ayan da zatasa babu yashiga neman aikin da zaiyi amma shiru gashi bawani tsufa yayi ba dan age ɗ'insa bazai wuce 45 ba.
Ana cik'in hak'a aka fara neman mai gadi a katan gidan nan sabida wanda yakeyi shima zai tafi garinsu dan ganin iyalinshi daya baro wata 3 kenan nan mutane suka cika gidan liman, danshi akasa ya nema yaya al-ameen babu ruwan shi bacci ne kawai yake agidan ya shirya yabarshi.cikin mane man harda Abban Falaq da yayan shi yaya bashir wanda kuma shine ya samu nasarar zama sabon mai gadi.
•••••••••••••••••••••••••••••>
Samun aiki yayiwa Abban Falaq wuyar samu nan yaji ana neman masu gyaran gidan, Allah ya temake shi ya samu aka ɗ'auke shi aikin,yasamu k'uɗ'i yaje ya nunawa ummi itama tayita murna dan tasan zata samu magani acikin k'uɗ'in.
wajan karfe biyar abba ya shiga gidan hannuwan shi ɗ'auk'e da ledoji guda biyu sallama yayi Falaq dake wanke wanke taɗ'ago taganshi da leda dasauri ta tashi tare da yimai oyo yo ta karbi leda guda ɗ'aya suka wuce d'akinda ummi take k'wance.
Sunnu da zuwa tayiwa Abba, yace yauwa matata ya jikin naki tace jik'i da sauki ya zauna kusa da ita a gefen gado k'allonta yake cik'e da so da k'auna dan ummi akwai kyau,hannun ta tasa mai lafiyar ta cire mai hular kanshi sukayi murmushi tare.
"Abba na buɗ'e nagani? Falaq ta faɗ'a tana k'allan shi,yace 'a'a kije ki gama aik'inki sannan munyi sallah sai a buɗ'e ko? Ba haka taso ba dan ita tama manta wanke wanke tak'eyi haka ta tashi tafita daga ɗ'akin tanata hasashin abindake cikin ledar.
Falaq yarinyace irin masu shigen surutun nan gata 'yar kubul kubul like pharty bb,shekarunta bazasu gaza shekara sha 12 ba fara ce saidai farin ya dishashe sabida rashin tsafta,tana da gashi irin mai laushin nan hakan yasa ko kitso akayi mata baya daɗ'ewa sannan k'wark'watar k'anta take binta ajikin kaya.
Bayan sunyi sallah falaq tace Abba a ɗ'akko ledar? umminta ne ta ce tace waike saurin mekike saikace kin aike shi,falaq ta turo bak'i kamar zatayi k'uk'a ganin haka abba yace ɗ'akko dama ai sakon nakine nan da nan ta saki rai tajanyo ledojin yaciro mata k'ayan da yasiyo mata ya bata.
Murna sosai Falaq tayi ta rungume Abba dake zaune yana kok'arin ciro atamfar ummi data hajiyarsu,Abba na maulidine k'asiyo min? yace ehh kina sonsu aiko da sauri tace ehh Abba nagode yace yauwa tunda k'inyi godiya bari a k'aramiki.
Yaciro wasu takallama irin yan ɗ'ari #350 ɗ'innan, Allah sarki ta dunga murna ganinsu take k'amar yan 10k, dama ai k'owa da irin arzik'in sa aduniya shikam babu abinda ya saimawa k'anshi raguwar kuɗ'in zaiyo musu chefanelan abinci da maganin ummi,dama Atine matar abokinsa tana ɗ'inki dan haka can zaikai na ummi hajiyarsa kuma yakai mata atamfar dan idan ya ɗ'in ka mata wani rigimar za'a.
••••••••••••••••••••••••••••>
Ummi ce ta fashe da kuka sosai ya k'wace mata hak'an yasa Falaq tasowa tazo k'usa da ita,
Ummi meyasa k'ike kuka? ciwan ki yake mik'i ciwo? ummi ta kasa magana hakan yasa Falaq cewa ummi nice ko Abba ne muka saki kuka?
girgiza kai ummi ta hauyi alamar a'a shikuwa Abba yasan abinda tak'ewa kuka dan haka yace da falaq taje ta k'wanta dare yayi,tace Abba ni banajin bacci saidai naje gidan hajiya yace to yabata atamfar yace tak'ai mata kafin yazo tace to takarɓ'a ta tafi za'aje a gayawa su farida ansai mata kaya.
Falaq na fita Abba ya maida hankalinsa ga ummi dake ta faman share hawaye da hannu ɗ'aya,gashi ta kasa k'allon shi yace, "Fatima k'in kasa rike kukanki da damuwarki ko? kullum saina yi miki magana indai t'sa'k'anina da hajiyane k'ici gaba da yimin addu'a in'sha Allahu babu mai rabamu sai mutuwa cuta lokaci ɗ'aya take shiga,sauki kuwa sai sanda Allah ya kawo shi k'ici gaba da hak'uri kina min addu'a babu mai rabamu k'inji" ummi tace to Allah yasa amma ni inajin tsoro.
Abba yace kidena tsoro kinsan ina sanki fatima soyayyarki tasa nakasa wani auren duk da bakida lafiya amma ai ina samun abinda ake bukata na auren ko?Ummi ta kalle shi,murmushi ta gani a fuskar shi saita ji kunyar shi hak'an yasa ta juya fuskarta gefe itama tana dariyar.
_Allah sarki Allah k'abarmu da masu k'aunar mu duniya walahira_
*hajja ce bch*👈🏻
Wow gaskiya wannan littafin yana da dadi sosai mun gode
ReplyDeletehttps://mynovels.com.ng/jiki-na-yake-so-complete-hausa-novel/