Monday, 24 April 2017

BABBAN SIRRI

*🏮🎀BABBAN SIRRI*🏮🎀
               2017

     *NA*
*K A S precious hajja ce*

*DEDICATED TO ummi aishat nd pharty b~b*

*Edited by supar star FUTHA LUV😍*

  _GABATARWA_

 _Da sunan Allah mai rahama mai Jin kai_

  _ina mik'a godiyata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai komai da yabani ikon rubuta wannan littafin nawa,Ya rabbil izzati alkhairin dake cikinsa Allah yaban lada,kura kuran dake cikinsa Allah ya yafe min._

 _Banyi wannan littafin nan nawa domin cin zarafin wani ba,in hak'an ta k'asance ayimin afuwa_

  _gaisuwa ta musamman ga yan uwana writers more especially :_

_💝💘stylish,@utan hajjiya,aneeluv,anisa didi,cute zarah,miss xoxo,pharty b~b,ummi aishat,@aishat ahmad,miss hafcy,harpsat rano,haneepa,munay,futha lurv,miss jh,billy giro,basma er lele,melody,jidda,al-amin,billy tabaco,ankah,mmn haneep,mmn ummul kairat,ummu ilham,sdy jegal,ja'o,faxfashion,leemcy,eshart,ayush,miemie bie,queen meimie,mmn uthman,ashar,bellosh,larmirat,pherty👯,aunty sis,@jiddah,ashat ilyas,luff,nd many others tnxs*_

*1*
    Tafe tak'e kan hanya sai sauri tak'e saboda Abbanta yanata gargaɗ'inta datayi sauri k'arta daɗ'e dan yanzu akeson maganin tana shan k'wanar dazata k'aita gida suka haɗ'u da Auwal tace gaskiya Auwalu karka tsaidani Abbana nacan yana jirana zaibawa ummina magani ta faɗ'a tana nuna mai maganin data siyo,Auwal yace "haba tawan k'ibari mana mu gaisa saik'i tafi k'wana biyu bana ganin ki duk na damu,tace nidai gaskiya tafiya zanyi ta murguɗ'a mai bak'i dan gaskiya ya fara tak'ura mata, ganin yaki bata hanya ga lokaci sai wucewa yak'e saita ruga da gudu.

Ta barshi da cizon yat'sa, Auwal k'enan yana bala'in sonta amma sai rashin kunya take mai,tun daga zaure take kwaɗ'a sallama k'amar wata mak'auniya harta k'aiga inda Abbanta ke tankaɗ'an garin tu
uwon da zaiyi musu,aikuwa saida yayi mata faɗ'an yakarɓ'i maganin yace ta k'arasa tankaɗen.

Wajan karfe 4:30pm Abba ya shiga gidan tare da sallama *Falaq* da ummi dake ɗ'aki suka amsa mai ya k'arasa ciki yana ganin Falaq babu ɗ'ankwali yasa hannu aljihu yaciro #50 "ungo k'ije gidan lauren nalami mai k'it'so tayi miki',kallan Abban nata ta shiga yi dan a rayuwa ta tsani k'it'so bataso taga ana taɓa mata kai indai ba......za'a cire mata ba.

Saida Ummi ta sak'e magana sannan ta karɓ'a tanata kuka ta fita daga gidan.

Tana tafiya tana masifa kamar zararriya sai jan gefe da gefen karshen mayafinta take wanda yayi dauɗ'a kamar daga bak'ar k'asa aka t'samoshi,tana shan k'wanar dazata k'aita gidan lauren nalami ta t'saya jikin wani gida mai bala'in k'yau duk garin babu gidan daya kaishi k'yau da tsaruwa, dai dai wata window irin me gless ɗ'innan ta t'saya tana k'arewa k'anta k'allo dama ka idarta ce indai zata biyo hanyar saita k"alli madubin nan,zahirin gaskiya ita kanta *Falaq* tasan tayi dauɗ'a tundaga fuskarta, k'ayan jikinta sunsha ɗ'inkin hannu k"anta kuwa sai a slow gashin nan yayi wata kala k'wark'wata kuwa kamar ita take siyarwa dan har bin jikinta take k"afarta kuwa duk ta fashe tayi futu futu data.

Tana gama ganin k'anta a madubi  ,ta wuce ta tafi gidan lauren nalami har addu'a take Allah yasa bata nan kota ce baz'ata samu dama ba,tun kafin tashiga zauren take rafk'a sallama harta k'arasa ciki laure na talgen tuwo Falaq na k'arasawa tace "laure zan samu k'it'so yanzu"? Da sauri laure tace Falaq mezai hana zaki samu mana,Falaq ta turo bak'i tace "kai laure aiki fa kike tayaya zakimin"?


Laure tace duk zan iyayi ina miki ina kula da aikin harmu gama,laure itake rufawa k'anta asiri dan Nalami babu abinda yake damun shi da ita sai dare.

Laure ta fito da kujera, comb da k'ifiya tacewa Falaq toho,haka Falaq ta zauna badan ranta yaso ba,ita kuwa laure kuɗin take so shiyasa zatayi mata haka akayi k'it'son babu wanke kan anayi ana tsintar k'wark'wata, a rayuwar falaq tana so taga ana ciro mata k'wark'wata tana k'ashewa kasss babu wanda yake k'yank'yami cikin su har aka gama sannan Falaq ta wuce gida.

Tana komawa gida abban ta ya gama tuwo da miyar k'ark'ashi,taje ta nunamai aikuwa yaji daɗ'i dan haka ya ringa shafawa yana yabawa kannata, taje ta nunawa umminta dake ɗ'aki a kwance tana fama da shanyewar ɓ'arin jiki,itama ta yaba saidai tayi mata faɗ'an rashin wank'ewar da batayiba,ashe rashin k'itson ba karamin rufawa Falaq asiri k'wark'watar tayi ba dan saida akayi suketa yawo a jikinta (lol).

Abba na shiga toilet ta arce gidan su uwani ta tafi k'awarta ce k'anwar Auwalu saurayinta nan sukayita wasan su har wajan sallar isha'i sannan tace zata tafi"

Abban zaune kusa da ummi yana bata tuwo tashigo da gudu harta kusa ɓ'arar da miyar tanata dariya,Abba ne yace waike Falaq yaushene zaki girma?sannan wakika tono? sarkin tonen faɗa, yafaɗ"a yana k'allanta.

Saiidata gama zama k'usa da k'wanan tuwon sannan tace Abba idirisu ne wai dan nace idirisuwa na lami shine ya biyoni zai dokeni,tana faɗ'a tana t'saka lomar tuwo a bakinta dan dama a gidan su  uwani bata ciba babu wanda yayi mata tayi,ummi dake kusa da ita tasa hannunta mai lafiyar ta doko Falaq tace bana hanaki wasa da maza ba wai meyasa bakida nutsuwa ne kodan kinganni kwance yasa kike irin waɗ"annan ɗ'abi'u to ki kiyayeni inba haka ba zan saɓa miki ummi ta karasa faɗ'a cikin zafin rai,shidai Abba ɓaice komai ba dan haka ya ɗ'eɓo tuwon yakai bakin ummi tace ta koshi dan har lokacin zuciyarta zafitake.

Abba ne yayi magana ganin Falaq ɗ'in kamar zatayi kuka dama kuma shine yake biye mata yana shagwaɓ'ata baya mata faɗ'a shiyasa batajin magana ko kaɗ'an saidai idan ummi ce,Abba yace wa ummi wai meyasa kikewa yarinyar nan haka? saikita mata faɗ'a batare da dalilaba to bana so kirabu da ita tayi abinda takeso kafin ace yau babu itah gaba ɗ'aya koni ko ke yana k'aiwa nan ya turawa Falaq ragowar tuwan yace ta cinye idan bata k'oshiba taje ta kara tace to tana k'allan ummi data haɗ'e fuska.

 🇳🇬 _happy new year_🇳🇬2017
*hajja ce*👈🏻✍🏻
Share:

0 comments:

Post a Comment

Blog Archive

Search This Blog

Contact Form

Name

Email *

Message *