Thursday, 27 April 2017

BABBAN SIRRI 3

*🏮🎀BABBAN SIRRI🏮🎀*


           *NA*
*K A S precious hajja ce*👈🏻

*Dedicated to ummi aishat nd pharty b~b*_

*Edited by super star FUTHA LUV*

*3*
     Ummin falaq ta cika da mamaki wai yau falaq ce tasan soyayya lallai sai sun kara sa ido akanta,musamma dataga irin yadda take shigewa Auwal, Auwal na fita ummi ta kalli falaq tace meye haɗin ki da auwal?

Sake rufe fuska falaq tayi wai ita nan kunya takeji,"haushi ya kara rufe ummi taji kamar ta tashi ta shaketa dan takaici suna haɗ'a ido ummi ta sakarmata harara sannan falaq ta shiga hankali ta tafara yan soshe soshe na rashin gaskiya.

Abban tane ya shigo tayi saurin tashi xuwa gurin shi tana mai sannu da zuwa tare da karɓ'ar ledar hannun sa  datake ta kamshin balangu.

Abba ya karasa inda ummi take ya zauna tare da kama hannunta yana matsawa cikin tsigar soyayya sukeyi ta yadda yar tasu da hankalinta yayi kan balangon da abbanta ya kawo musu baxata ganeba.

kusa da kunnan ummi abba ke mgn a hankali"bari naje na samo miki kankana kishi yau akwai aiki dan ina bukatarki cikin jikina gaba ɗayan su biyun suka k'washe da dariya harda falaq dabata san me sukewa dariyar ba amma saidata dara itama.

Falaq ta gama juye musu wake da shinkafar da abba ya kawo ta xuba balangun akai sai abba yace bari yaje yadawo yanxu,"abba ina kuma xaka? Falaq ta faɗ'a dan ta k'agara taci naman kuma duk tare suke cin abinci wanda Abba ke bawa ummi da kanshi.

"Abba yace bari yanxu zan dawo ya faɗa yana fita daga d'akin"

Ranar dai su falaq ansha daɗi anyi kwanan farin ciki,su abba ma 🙊.......

k'yak'yawan saurayine  son k'owa k'in wadda ta rasa ɗ'an k'imanin shekara ashirin da biyar,a hankali yake fitowa daga cikin k'atafaran gidan, cike da kasaita har xuwa wajan motar da aka gama wanketa aka fitomai da ita waje.

Dak'a ganshi k'aga balarabe sak yana sanye da jallabiya milk colour sai ɗ'aukar ido takeyi ya k'arasa wajan motar sai zabga kamshi yake kamar anyi wankan turare a gurin ya buɗ'e ya shiga ya zauna a driver seat yajawo seat belt yasa.

Wayar shi ya ɗ'auka yana danne danne a jiki kome yak'eyi ban saniba sabida na hango muku falaq.

 Falaq ta dawo daga siyan kosai da koko tana shawo k'wanar dazata kaita gida ta hango wata lafiyayyar motar fara sai ɗ'aukar ido take.Cikin sauri ta taho dan kuwa saita kalli madubi tukunna.

Tana zuwa ta fara gyare gyare a jikinta sai wani jujjuyawa takeyi a gaban glass ɗ'in.

Arfat na kokarin saka key yaganta sai feleke take kasancewar glass ɗ'in motar bakine ita bata ganin shi,shine yake ganinta.

Tsayawa yayi yana kallon ikon Allah da baya k'arewa yafara tunanin kodai tana da jinnu  ne shiyasa take ta kallon  madubi, a hankali ya zura key ɗ'in ya tada motar yana kallanta.

Jin motar ta kunnu yasa cikin Falaq murɗawa tareda xaro idanuwa tana kara makale ledar k'osan da kofin kokon jin ta mutu ta fara kukuku yasata ɗaga xaninta sai gudu.

Mamaki yasa ke k'ama shi dan ganin abun gudu baya mata wuya ya girgixa k'ai tare da taɓ'e bak'i yatada motar  ya wuce cikin gari.

Da gudu ta shiga gida ta kankame ummi tana haki,cikin sauri da ruɗ'ani ummi ke tambayar me ya falaq na nuna mata kofa da hannu dan ta k'asa magana,Abban tane ya fito daga bayi yaji ummi nata tambayar Falaq ko lafiya,  karasowa kusa da ita yayi saida ya bari ta dawo cikin hank'alin ta sannan ya tambayeta kumeye.

Tana gama gaya mai yace wato yauma k'inje k'in tone shi? Wai me yasa kina girma amma k'in xama sha'sha'sha? Bana san k'ik'ara ko k'alli kofar gidan bare k'ileka mai ɗ'aki k'o motarsa k'inajina? Abba ya faɗa yana t'sareta da ido k'afin tace to tana cokaro baki k'amar zatayi kuka.

wajan k'arfe 4:00pm salama k'anwar Abban Falaq ta shigo gidan ta k'arasa har ɗ'aki inda ummi ke k'wance,tunda naga kallon da salama tak'eyiwa ummi nasan bada shiri tazo gidan ba jinayi tana cewa to asartacceya makira nakasarshi walhy ni kurwata ɗ'aci gareta nafi k'arfin k'i nesa ba k'usa ba.

Kuma walahi dole k'ibar yaya ya kara aure, mata sai shegen iyayi babu abinda k'ike k'aramai sai rama da asara kullum k'ina k'wance bakida mammora aikin banxa,shikuma yayan nan duk yabi yawani damu k'anshi akanki sai kace wata uwar shi. Ita dai ummi bata ce k'alaba hasalima murmushi ne kwance a fuskarta kamar bata damu da k'alaman salama ba harta yi tagama batace mata komai ba, wannan ya k'ara tunxura salama tadinga masif k'amar sabuwar k'amu, ta fita tana masifa dan dama zuwatayi taci mata xarafi.

"Allah sarki ummi sai yanxu ta samu damar yin k'uk'a mai ratsa xuciyar wanda ke saurare"

Sallamar Falaq data dawo daga makarantar allo shiyasa tayi saurin share hawayen nata tayi k'amar tana bacci.

Falaq ta k'arasa wajan ummi ta zauna k'usa da ita tana k'are mata kallo. umminta me kyau amma bata tafi tana zancen zuci taga idon ummi na k'iftawa da sauri tayi dariya tace Allah ummi bakiyi bacci ba ga idonki yana motsi,maganar tabawa ummi dariya hakan yasa taɗ'an yi dariyar tace ja'ira k'inzo kinsani gaba ai dole na k'asa bacci sukayi dariya gaba ɗ'ayan su.

Jin an shigo anata yi musu ball da kaya a tsakar gida yasa Falaq fita da sauri dan ganin meyi musu wannan aika aikar, sallau dillalin gidaje ne ya shigo yana musu ɗ'ibar albarka yana ganin Falaq yace ke ina Abban? ki tace bayanan.

Nan yaringa masifar yau sai an bashi k'uɗ'in hayar shi ko k'uma subar mishi gidan,dan yagaji da gafar sa ɓ'ega kahoba.

Ummi sallaune kuma sai watsar mana da k'aya yakeyi Allah zanje nayimai rashin k'unya, falaq ne dake tsaye take gayawa ummi hak ranta ɓ'ace dai dai nan Abba ya dawo yaga abinda ake mishi cikin muhallinsa.

Ya kalli sallau dillali cike da mamaki da ɓ'acin rai yace bana ce kadena shigar mini ciki ba kodan kana  ganin gidan a k'ark'ashinshi ka yake?


_🇳🇬happy new month🇳🇬_2017
```hajja ce```👈🏻✍🏻
Share:

1 comment:

Blog Archive

Search This Blog

Contact Form

Name

Email *

Message *